ABNA24 : Shugaba Idriss Deby Itno, wanda ya shafe sama da shekaru 30, yana mulkin kasar, na fafatawa da ‘yan takara shida a zaben domin neman wani wa’adin mulki na shida.
Kimanin ‘yan kasar miliyan 7,4 ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben.
Saidai wani bangare na ‘yan adawan kasar sun janye daga zaben, tare kuma da kira ga jama’ar kasar su kaurace wa zaben.
Jiya Asabar dai sojojin kasar sun jefa tasu kuri’a a zaben.
342/