ABNA24 : Osman Dubbe ya kara da cewa shuwagabannin yankuna masu cin gashin kansu na Puntland da kuma Jubbaland ne suka hana ci gaba a taron, inda suka bayyana cewa ba sa son magadishu ta shiga cikin al-amuran zabe a yankunansu. Dubbe ya kammala da cewa Puntland da Jubbaland ba sa son gwamnatin tarayyar kasar a Magadishu ta shirya zabe a yankunansu kamar yadda yarjejeniyar 17 ga watan Satumba da kuma 16 ga watan Fabrairu suka bukaci a yi hakan ba.
Halaccin gwamnatin shugaba n kasar Somalia na yanzu dai, wato Abdullahi Faarmajo ya kare tun watan Fabrairun da ya gabata, sannan jam’iyyun ‘yan adawa suna zargin shugaban da son ta zarce a kan kujerar shugabancin kasar ba tare da zabe ba.
Shugaban Jubbaland dai, Ahmed Madobe ya ce baya son Mogadishu ta tsoma baki a zabubbukan da za’a gudanar a yankinsa, don haka shi yana son ya zabe ‘ya’yan kwamitin zabe na lardinsa da kansa. Masana dai suna ganin rarrabuwar kai dake tsakanin yan siyasar kasar ta Somalia dai zai bawa kungiyar yan ta’adda ta Alshabab damar kara tashe tashen hankula a kasar.
342/