ABNA24 : Rahotannin farko sun ambaci cewa wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 18, sai dai daga baya adadin ya kai 40, yayin da wani adadi mai yawa ya jikkata.
Mazauna yankin da kuma majiyar MDD sun shaidawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; An yi amfani da manyan makamai da gurnet-gurnet wajen kai wa juna hari a tsakanin kabilun biyu na Larabawa da Masalit.
A farkon wannan shekarar a cikin watan Janairu, an yi fada a yankin wanda ya ci rayukan mutane 129.
Tun dai gwamantin kasar ta Sudan ta sanar da kafa dokar hana fita, sannan kuma ta aike da babbar tawaga zuwa yankin domin haduwa da shugabannin kabilun biyu domin tattauna hanyoyin zaman lafiya.
An fara samun rikici ne a yankin na Darfur bayan da kabilun da ba larabawa ba su ka yi wa gwmanatin Khartum tawaye a 2003. A wancan lokacin adadin mutanen da aka kashe sun kai 300,000, yayin da wasu miliyan 2.5 su ka zama ‘ yan gudun hijira.
342/