ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Anadolu na ƙasar Turkiyyan ya bayyana cewar ana tsare da tsoffin manyan sojojin ne a ci gaba da binciken da babban mai shigar da ƙara na ƙasar Turkiyyan ya ke yi ne kan sanarwar da suka fitar. Kamar yadda mai shigar da ƙarar ya buƙaci wasu huɗu daga cikin waɗanda ake zargin da su kai kan su wajen ‘yan sandan birnin Ankara ba tare da an tsare su ba saboda yanayin tsufa da suke da shi.
Wasu kafafen watsa labaran Turkiyyan sun ce ana zargin mutanen ne da abin da mahukuntan suka kira ‘amfani da ƙarfi da tashin hankali wajen kawar da tsarin da ke gudanar da ƙasar’.
An tsare mutanen ne kwana guda bayan da wasu manyan sojojin ruwan da suka yi ritaya su 104 suka fitar da wata wasiƙa da suke nuni da rashin jin daɗinsu da yadda lamurra suke gudana lamarin ya fuskanci kakkausar suka daga fadar shugaban ƙasa, wacce ta bayyana hakan a matsayin wani ƙoƙarin juyin mulki.
342/