5 Afirilu 2021 - 08:37
An Kara Farashin makamashi A Kasar Sudan

Gwamnatin kasar Sudan ta bada labarin kara farashin makamshi a kasar a cikin shirin hukumar na dauke tallafin da gwamnatin take bawa makamashi a kasar.

ABNA24 : Jaridar Sudan Tribun ta kasar Sudan din ta bayyana cewa gwamnatin kasar ta kara farashin man ne dai-dai da tashin farashin makamashin a kasuwannin duniya. Labarin ya kara da cewa an kara farashin man fetur ne daga dalar kasar Sudan 122 zuwa dalar kasar Sudan 150, a yayinda aka kara farashin man desel kuma daga dalar Sudan 115 zuwa dalar sudan 125 zuwa.

Kamfanin man makamashi na kasar Sudan ne ya bada wannan sanarwan tun ranar Alhamis, ya kuma kara da cewa sabon farashin makamashin zai fara aiki tun rannan.

Amma mataimakin shugaban kwamatin tattalin arziki na gwamnatin rikon kwarya na kasar ta Sudan Adil Khalafallah, yay i allawadai da Karin farashin makamashin, ya ce wannan ya nuna cew agwamnatin kasar bata damu da matsalolin da Karin farashin zai jawowa mutanen kasar ba.

Khalafallah, ya fadawa Sudan Tribune kan cewa manya-manyan kasashen duniya wadanda gwamnatin Sudan ta karbi basussuka daga wajensu, su ne suke takura mata don ta dauki wannan matakin.

342/