5 Afirilu 2021 - 08:21
Indonasiya: Zaizeyar Kasa Da Ambaliyar Ruwa Sun Kashe Mutane Fiye Da 50 Wasu Da Dama Sun Bace

Zaizeyar kasa da kuma ambaliyar ruwa sanadiyyar ruwan sama sun yi sanadiyyar halakar mutane fiye da 50 a kasar Indonasia.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto majiyar kungiyar bada agajin gaggawa ta kasar tana cewa a lardin ‘Gabacin Nusa Tenggara, sun gano gawakin mutane 35 sannan wasu mutane 5 kuma sun ji rauni bayan da laka ta binne gidaje a lardin.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar ta ce mutane fiye da 100 ne suka bace ko ba san inda suke ba bayan ruwan sama da kuma zaizeyar kasar.

Kasar Indonesia dai tana da tsibirai 17,000 inda mafi yawansu cike da duwatsu da tsaunuka.

An saba rasa rayuka sabuda ambalin ruwa a kasar Indonasia a ko wace shekara saboda yawan ruwan sama da kuma yanayin kasar. A cikin watan jenerun da ya gabata ma mutane 40 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar zaizayar kasa a tsibirin Java na kasar.

342/