ABNA24 : Jiya Litini, ne aka soma shirin a Yamai babban birnin kasar da allurar rigakafin cutar ta korona da kasar China ta tallafawa kasar da ita.
Firaministan kasar Brigi Rafini da mukaddashin ministan harkokin kiwon lafiyar jama’a Ahmed Boto, sun halarci bikin fara alluran rigakafin COVID-19 da aka yi a wannan rana, inda aka fara yiwa firaminista Rafini allurar rigakafin.
A jawabinsa bayan karbar rigakafin, firaministan ya ce, ya bukaci al’umma da su karbi alluran rigakafin cikin himma da kwazo.
A nasa bangare, ministan lafiyar kasar ta Niyar Ahmed Boto ya ce, da farko, za a yiwa ma’aikatan lafiya, da masu aikin tsaron kasa, da tsofaffi masu shekaru sama da shekaru 60, da wadanda suke fama da wasu cututtuka, kamar ciwon suga, da cutar kanjamau da sauransu rigakafin.
A ranar 21 ga watan ne Nijar ta karbi tallafin farko na alluran riga kafin cutar korona daga kasar China.
Nijar dai ba ta daga cikin kasashen da cutar korona ta yi wa mummunan ta’adi idan aka kwatantan da sauren kasashen duniya.
342/