25 Maris 2021 - 13:47
Nijar : An Ranstar Da Seyni Omaru, A Matsayin Sabon Shugaban Majalisar Dokoki

A Jamhuriyar, sabon shugaban majalisar dokokin kasar malam Seyni Omar, ya yi rantsuwar kama aiki a gaban kotun tsarin mulkin kasar.

ABNA24 : A jiya Talata ne takwarorinsa suka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Shi kadai dama ya tsaya a neman shugabancin majalisar.

Dan shekara 70, dama ya taba rike wannan mukami a loakacin mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Mamadu tanja, daga watan Nuwamba 2009 zuwa Fabarairu 2010.

Malam Seyni Omar, shi ne wanda ya zo na uku a zaben shugabancin kasar zagaye na farko a watan Disamba da ya gabata, kafin daga bisani ya goyi bayan dan takarar jam’iyyar PNDS tarayya mai mulki Bazoum Mohamed wanda ya lashe zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

342/