ABNA24 : Sakamakon zaɓen dai yana nuni da shugaba Nguesso ɗan shekaru 77 a duniya wanda kuma yake mulkin ƙasar tun shekaru 36 da suka gabata yayi fintinkau wa babban abokin karawarsa Guy Brice Parfait Kolelas wanda ya mutu kwana guda bayan gudanar da zaɓen sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.
Sakamakon zaɓen dai ya nuna cewa Mr. Kolelas ɗin ya samu kashi 7.84 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa ɗin ne.
Wannan nasara da aka sanar shugaba Nguesso ɗin ya samu daman wata nasara ce da tuntuni ake zaton zai samu ganin irin yadda ‘yan adawa suka ƙaurace wa zaɓen.
Ɗaya daga cikin ‘yan takarar da suka sha kaye a zaɓen Mathias Dzon ya ce zai kai ƙara kotun kudnin tsarin mulki ta ƙasar kan ta soke zaɓen bisa la’akari da yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya nuna cewa wajibi ne a soke zaɓen matuƙar dai ɗaya daga cikin ‘yan takaran ya mutu ko kuma ya gagara kaɗā kuri’a, sai dai kuma hukumar zaɓen ta ce ɗan takaran da ya mutun wato Mr. Kolelas ya mutu ne bayan kaɗa kuri’ar.
342/