ABNA24 : A jiya ne shugaban kasar ya karbi tallafin da ya kunshi kwaba 400,000 na riga kafin SINOPHARM daga hannun jakadan kasar ta Sin a Nijar.
Shugaban kasar ta Nijar, ya sanar cewa za’a fara yi wa jama’a riga kafin a ranar Asabar mai zuwa 27 ga wata.
A cewar Shugaba Issoufou, bayan samun wannan gudummawa, Nijer za ta fara aikin riga-kafin cutar COVID-19 a ranar Asabar mai zuwa, inda za a bada fifiko ga ma’aikatan lafiya, da mutane masu fama da wasu cutuka da kuma masu yawan shekaru, da jami’an tsaro.
Wannan dai shi ne karon farko da Nijar ta karbi riga kafin cutar korona.
Kawo yanzu, Nijer tana da jimillar mutane 4918 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, yayin da cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 185, kana mutane 4538 sun warke daga cutar.
342/