22 Maris 2021 - 08:21
Kungiyar Mi Yetti Allah Ta Musanta Zargin Gwamnatin Benue Na Kai Masa Hari

Shugaban Kubgiyar Miyetti Allah Kawtal hoore ta Fulani a tarayyar Najeriya Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya karyata kalaman Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom na cewa makiyaya ne suka kai masa hari a lokacinda yake wucewa a kan wani bababn titi a cikin jihar.

ABNA24 : Lamiido Fulbe Bello bodejo ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook da kuma Instagram a yau Lahadi ya kuma kara da cewa:

“Kalaman Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom na cewa makiyaya sun kai masa Hari a Hanyar Makurɗi Zuwa Gboko Karya ce zogiranta” Bodejo ya, gwamnan ya na nuna kiyayya ne ga Fulani makiyaya da kuma Kungiyar Miyetti Allah Kawtal hoore ne, wacce ta staya don ganin ta kalubanci haramtarciyar dokar kabilanci da wariya da ya kafa a Jihar, saboda haka ne yake shirga kariya wacce zata batawa Fulani makiyaya Suna, inda shi kuma zai sami goyon bayan gwamnatin Tarayyar kasar.

Bodejo ya kammala da cewa, babu wani Fulani da ya isa ya je yankin da gwamnan yake cewa na kai masa hari a cikinsa, tun bayan kafa dokar wariyan da yay i a shekara ta 2018.

342/