22 Maris 2021 - 08:09
An Kawo Karshen Yakin Neman Zabe A Jamhuriyar Congo

Yakin neman zaben shugabar kasa a jamhuriyar Congo ya zo karshe a ranar Juma’ar da ta gabata. kuma masu kada kuri’a za su nufi cibiyoyin zabe a yau Lahadi domin zabar shugaban kasa wanda zai yi shekaru shida akan karagar mulki anan gaba.

ABNA24 : Shugaba Denis Sassou Nguesso mai shekaru 77 a duniya,yana sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na 4 a karkashin taken da yake bayarwa na cewa; Za mu ci gaba da yunkuri wajen gina kasa.”

Wanda ake ganin zai kalubalanci shugaban kasar shi ne Guy Brice Parfait, sai kuma Mathias Dzon.

Wasu ‘yan takarar dai sun hada da Joseph Kingnoumbi.

A yau ne dai ake sa ran za a kada kuri’ar zaben shugaban kasar.

342/