ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar Muhammad Al-manfi ya na fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a tashar talabijin ta kasar.
Al-manfi ya kara da cewa majalisarsa za ta yi kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a kasar Libya sannan mutanen kasar a cikin ‘yenci zasu kafa tsarin democradia wacce za ta lamuncewa ko wani dan kasar hakkinsa.
A wani taro, wanda majalisar dokokin kasar ta Libya ta gudanar a birnin Sirt a ranar Laraban da ta gabata ce wakilan majalisar 132 suka zabi Al-manfi sabon shugaban riko wanda zai hada kan mutanen kasar ya kuma azata kan turbar democradiyya.
342/