9 Maris 2021 - 12:14
​Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou Ya Lashe Kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issofou ya lashe kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim dake dauke da Dala miliyan 5 saboda yadda yaki amincewa ya sauya kundin tsarin mulkin domin cigaba da zama a karaga kamar yadda wasu shugabannin kasashen Afirka ke yi.

ABNA24 : Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, gidauniyar tace shugaba Issofou ya gudanar da jagoranci na gari wajen shawo kan matsalolin da suka addabi jama’a irin su talauci, yaki da ‘yan ta’adda da kuma fari.

Shugaban kwamitin bada kyautar Festus Mogae yace shugaban ya yi nasarar rage yawan jama’ar kasar dake fama da talauci daga kashi 48 da aka sani shekaru 10 da suka gabata zuwa kashi 40.

Mogae yace duk da kalubalen da ke gaban shugaban, Issoufou ya cika alkawarin da ya yiwa al’ummar Nijar na shata wa kasar makoma mai kyau wajen shirya zaben da ya samar da wanda zai gaje shi, wanda shi ne irin sa na farko tun bayan lokacin da kasar ta samu ‘yanci daga kasar Faransa sama da shekaru 60 da suka wuce.

342/