ABNA24 : Majiyoyin sun yi ishara da cewa, kasashen turai sun fahimci bayanin shugaba Rauhani da kuma Jawad zarif suka yi kan sabbin matakai dangane da batun tattaunawa tsakanin Amurka.
Bisa abin da majiyoyin suka ambata, sabbin matakan za su zo ne kawai idan Amurka ta janye dukkanin takunkumanta a kan Iran, a lokacin Iran za ta koma yin aiki da bangarorin yarjejeniyar nukiliya da ta jingine yin aiki da su.
Sannan kuma idan har akwai wani batu da bangarorin biyu za su tattauna a a kansa, dole ne ya zama kan batun yarjejeniyar nukiliya ne kawai, wanda ya hada sauran bangarorin yarjejeniyar, wato, Rasha, China, Jamus, Burtaniya da kuam Faransa.
342/