8 Maris 2021 - 10:57
Ministan Harkokin Wajen Irlande Na Ziyara A Tehran

Ministan harkokin wajen kasar Irlande, Simon Coveney, ya fara wata ziyara a birnin Tehran na Iran.

ABNA24 : Yayin ziyara tasa Mista Coveney, ya gana da takwaransa na Iran, Muhammad Jawwad Zarif.

Bangarorin biyu sun tattauna kan alakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma batutuwan da suka shafi yankin dama duniya baki daya.

A hannu daya kuma kasashen biyu sun tattauna game da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Ministan harkokin wajen kasra ta Irlande, ya bayyana ziyarar da mai cike da mahimmanci a daidai lokacin da kasarsa ke shirin aike da jekada a birnin Tehran da kuma shirin bude offishin jekadanci kafin nan da shekarar 2023.

Irlande ta bakin ministan harkokin wajenta ta ce tana ci goba da goyan bayan yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekarar 2015, kuma tana mai fatan dukkan bangarorin da yarjejeniyar ta shafa su mutunta alkawarin da suka dauka game da yarjejeniyar.

342/