ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa jirgin ‘kamfanin Emirate’ da ya kawo alluran ya iso kasar ne da misalign karfe 12 na rana, kuma wannan ya sanya Najeriya a matsayin kasa ta 3 a nahiyar Afirka wacce ta sami alluran riga kafin cutar ta Covit 19 na COVAX, bayan kasashen Ghana da Ivory Coast.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO da wasu kawayenta ne karkashin shirin nan na COVAX suka samar da alluran ga wadannan kasashen Afirka.
Shirin COVAX dai ya na nufin samarwa kasashe 92 a duniya, masu matsakaici da marasa karfi a duniya alluran riga kafin cutar ta korona kimani biliyon 2.
Alluran riga kafin cutar kimani miliyon 4, wadanda Najeriya ta karba a yau dai na kamfanin magunguna na Oxford-AstraZeneca ne.
342/