ABNA24 : Isa Dulkun wanda aka Haifa a yankin Xinjiang, wanda mafi yawan mazaunan yankin musulmi ne ‘yan kabilar Uyghur, ya bayyana cewa, daukar matakan nuna musu wariya da mahukuntan China suke yi ba sabon lamari ba ne, amma dai a cikin shekarun baya-bayan nan lamarin yafi tsananta, sakamakon daukar matakai da ake na hana su gudanar da harkokinsu na addini, bisa wasu hujjoji marasa tushe.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, ana kiransu da kabilar marasa rinjaye a kasar China, ya ce su ba marasa rinjaye ba ne, domin kuwa su ‘yan kasar China ne kamar kowa, suna da hakki kamar kowane mutum a kasar a matsayinsa na dan kasa, to amma dukkanin matsalolin da suke fuskanta da banbancin da ake nuna musu, hakan na faruwa ne saboda su musulmi ne.
342/