ABNA24 : A cikin sakon nasa wanda ya aike zuwa ga zaman taron kungiyoyin dalibai musulmi a jami’ion kasashen turai karo na 55, Imam Khamenei ya jadadda muhimmancin irin gudunmawar da matasa musamman dalibai da suka yi karatu a fagagen ilimomi daban-daban suke bayarwa domin ci gaban al’umma da kuma gina ta.
Ya ce abin da ya faru a wannan lokaci kimanin shekara guda ya zuwa na bullar cutar corona da kuam watsuwarta a duniya, ya nuna yadda matasa masu himma suka bayar da gudunmawa suke ci gaba da bayarwa a bangarori daban-daban na kiwon lafiya.
Jagoran ya ce, matasa masu karatu a bangarori na ilimi a jami’oi daban-daban, wannan babbar dama ce a gare su, wadda ya kamata su yi amfani da ita domin samun duk wani ilimi da zai ba su damar taimakon al’umma da kuma ci gabanta a dukkanin bangarori.
342/