ABNA24 : Jakadan na Iraki a Vatican ya kara da cewa; Paparoman yana son karfafa hanyoyin tattaunawa a tsakanin addinai da kuma rayuwa a tare cikin zaman lafiya da fahimtar juna.
Har ila yau Paparoman da zai gana da Ayatullahi Sistani zai tattauna da shi akan hanyoyin fada da tsattsauran ra’ayi da ta’addanci irin na kungiyar Da’ish.
Wani sashe na bayanin jakadan Irakin a fadar “Vatican” ya kunshi cewa; Paparoman zai yi kira ga dukkanin ‘yan siyasar Irakawa da su rungumi tattaunawa domin karfafa yarda da juna a tsakaninsu.
342/