11 Faburairu 2021 - 13:15
Lebanon: Hariri Ya Gana Da Macron Inda Suka Tattauna Abinda Ya Hana Kafa Gwamnati A Kasar Lebano

Firai ministan kasar Lebanon Sa’adul Hariri wanda yake ziyarar aiki a birnin Paris na kasar Faransa ya tattauna da shugaban kasar Emmanuel Macron dangane da dalilan da suka hana shi kafa majalisar ministoci a kasar.

ABNA24 : Jaridar “Annashrah” ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Hariri ya fadawa Macron cewa ya na kokarin kyautata dangantakar kasarsa da sauran kasashen Larabawa don sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Lebanon wanda yake kara rauni.

Tun ranar 22 ga watan Octoban da ya gabata ne aka dorawa Sa’addul Hariri nauyin kafa gwamnati a kasar ta Lebanon, amma ya kasa yin haka saboda sabadi tsakaninsa da kuma shugaban kasar ta Lebanon Michele Aun kan wadanda za’a nada a mukaman ministoci da kuma yadda gwamnatin za ta kasance.

Gwamnatin kasar Faransa dai ta yi alkawarin za ta bukaci kasashen Turai su tallafawa kasar ta Lebanon wajen tada komatsar tattalin arzikin kasar, musamman bayan facewar da ta auku a tashar jiragen ruwa na birnin Beirut a cikin watan Augustan da ya gabata.

342/