30 Janairu 2021 - 13:30
​Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Musunta Rahoton Karuwar Cin Hanci Da Rashawa

A cikin wani martani da ta mayar, fadar Shugaban Najeriya ta musunta rahoton Transparency International, wanda ya nuna cewa an kara samun koma-baya a Najeriya ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa.

ABNA24 : A cikin rahoton dai an bayyana cewa, Najeriya na a sahun gaba na kasashen da aka fi karbar rashawa da cin hanci da rashawa, bayan da aka alkalumman suka karu a cikin shekara ta 2020 da ta gabata.

Mai magana da yawun shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya fito ya musunta wanna rahoto, inda sun fara yin nazari kan yadda aka shirya rahoton, da kuma hanyoyin da aka bi wajen harhada alkalumman, har aka samu wannan sakamako, wanda ya nuna cewa a halin yanzu dai Najeriya ita ce kasa ta biyo a nahiyar Afirka ta fuskacin ayyukan cin hanci da rashawa.

Kungiyar Transparency International, ta fitar da jadawalin kasashen da aka fi cin hanci da rashawa a cikin shekarar 2020, wanda kuma ya nuna cewa Najeriya ta kara samun koma baya a wannan bangare a cikin wannan shekarar da ta gabata.

Rahoton dai ya ce matsalar ta kara muni ne matuka a tsakanin shugabanni da kuma ma’aikatan gwamnati, inda a shekarar 2020 Najeriya ta samu maki 25 cikin dari ne, wato kasa da maki 26 da ta samu a cikin shekara ta 2019, sai gwamnatin shugaba Buhari na ganin cewa ta yi gagarumin aiki da kuma samun babbar nasara wajen dakile ayyukan cin hanci da rashawa a Najeriya.

342/