ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, gwamnatocin kasashen Iran da Qatar suna gudanar da zaman taro na hadin gwiwa a yau a kan harkokin tattalin arziki a tsakaninsu a birnin Isfahan, tare da halartar manyan jami’ai daga bangarorin biyu.
Daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar Qatar da ke halartar taron akwai ministan harkokin kasuwanci da sana’oi na kasar Qatar, Ahmad Al-kawari, sai kuma wasu daga cikin jami’an kasar da suke tare da shi a cikin tawagar tasa.
A bangaren Iran kuwa ministan makamashi da wutar lantarki, gami da manyan jami’ai daga ma’aikatun harkokin kasuwanci, tattalin arziki, ma;aikatar harkokin waje, gami da wasu shugabannin kamfanonin Iran ne suke halartar taron.
Babban abin da wannan taro yake mayar da hankali a kansa shi ne, fadada hanyoyin kasuwanci tsakanin kamfanoni, da kuma ayyuka a bangaren makamashi tsakanin Iran da Qatar.
Kasashen Iran da Qatar dai suna da kyakkayawar alaka ta siyasa, tsaro, tattalin arziki kasuwanci da kuma ayyuka a bangaren makamashi.
342/