21 Nuwamba 2020 - 16:09
Mutane 8 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Hare-Haren Rokoki A Birnin Kabul Na Afghanistan

Rahotanni daga kasar Afghanistan sun ce alal akalla mutane 8 sun rasa rayukansu kana wasu kuma da dama sun sami raunuka sakamakon hare-haren rokoki da aka kai yanki mafi tsaro na birnin Kabul, babban birnin kasar inda da dama daga cikin ofisoshin jakadancin kasashen duniya da kuma wasu ofisoshi na kasa da kasa suke.

ABNA24 : Yayin da yake sanar da hakan, kakakin ma’aikatar cikin gidan kasar ta Afghanistan, Tariq Arian ya ce ‘yan ta’addan da suka kai harin sun harba wadannan rokoki ne daga kan wata mota wacce suka yi amfani da ita wajen kai harin.

Kakakin ya ce bisa ga bayanai na farko-farko da aka samu, hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 da kuma raunana wasu 31 baya ga hasarar dukiyar da aka yi.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin.

Kungiyar Taliban da take yakar gwamnatin Afghanistan din ta ce ba ta da hannu cikin wannan harin.

Yayin da yake sanar da hakan, Kakakin kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya ce kungiyarsu ba ta da hannun cikin wadannan hare-hare da aka kai Kabul da rokoki.

342/