5 Nuwamba 2020 - 13:18
​Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Isa Venezuela Don Ziyarar Aiki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zareef ya isa birnin Caracas babban birnin kasar Venezuela a jiya Laraba, inda ya sami tarbar tokwaransa na kasar Venezuela Jorge Arreaza.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labarai na gwamnatin kasar Venezuela AVN, yana fadar haka, ya kuma kara da cewa bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi kasashen biyu da dama.

A cikin yan watannin da suka gabata ne dai, kasar Iran ta tura jiragen ruwa dauke da makamashi zuwa kasar ta Venezuela don kawo karshen karancinsa a kasar wanda takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar suka haddasa.

Labarin ya kara da cewa Zareef zai ziyarci kasashen Cuba da Bolivia bayan Venezuela, inda ake saran zai halarci bukin rantsar da sabon shugaban kasar Bolivia Luis Arce.

342/