29 Oktoba 2020 - 13:36
​Yemen: An Gano Wadanda Suka Kashe Ministan Wasanni A San’a

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin San’a a kasar Yemen ta sanar da cewa, an gano wadanda suke da hannu wajen kisan ministan matasa da wasanni.

ABNA24 : Tashar almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin San’a a kasar Yemen ta sanar da cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar gano wadanda suke da hannu wajen yin kisan gilla a kan ministan matasa da wasanni Hassan Zaid.

Bayanin ya ce bayan kisan gillar da aka yi wa ministan a ranar Talata da ta gabata, a cikin kasa da sa’oi 24 jami’an leken asiri na gwamnatin san’a sun gano wadanda suka aikata kisan.

A lokacin da aka kai samame a inda suke domin cafke su, an yi musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro, kuma a nan take aka halaka daya daga cikinsu mai suna Yasir Muhammad, wanda yana daga cikin wadanda suka bude wa ministan wuta, yayin da kuma aka kame daya.

Mutanen biyu dai su ne suka bude wa ministan wuta aranar Talata alokacin da yake tuka motarsa a cikin birnin San’a tare da diyarsa, inda ya rasa ransa, yayin da kuma diyarsa ta samu munanan raunuka.

342/