ABNA24 : Majiyar muryar JMI ta nakalto Muhsen Rizayi yana fadar haka a yau Laraba a lokacinda yake ganawa da shugaban rundunonin masu gwagwarmaya a kasar Iraki, wadanda ake kira Hashdu, Sheikh Akbar Alkaabi a nan birnin Tehran.
Muhsen Rizayi ya kara da cewa, gwamnatin kasar Amurka ta na son kasashen larabawa makha’inta su fuskanci kawancen masu gwagwarmaya a yankin, amma Amurka ba ta da zabi in banda ficewa daga yankin.
Har’ila yau Amurka tana son maida HKI a matsayin wakilinta a yankin Asia ta kudu wanda hakan ma ba zai yu ba.
Rizae ya kammala da cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraqi su na kara karfi duk tare da matsalolin da kasar Amurka take haddasu a kasar.
A na shi bangaren Sheikh Kaabi ya bayyana cewa Amurka ta na kokarin ganin ta haddasa yakin cikin gida a kasar Iraki wanda zai ba ta damar rarraba kasar nan gana.
Shugaban dakarun Nujabaa ya kammala da cewa ofishin jakadancin Amurka a Bagdaza cibiyar yada fitina a kasar Iraki kawai.19.
342/