26 Oktoba 2020 - 18:44
Firayi Ministan Pakistan Yayi Tir Da Shugaban Faransa Saboda Kwaɗaitar Da Kyamar Musulunci Da Yake Yi

Firayi ministan ƙasar Pakistan, Imran Khan, yayi kakkausar suka ga shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron saboda kwaɗaitar da kyamar Musulunci da yake yi ta hanyar ‘sukar Musulunci’ da yake yi da kuma kare buga zanen ɓatanci da ake yi wa Manzon Allah (s.a.w.a).

ABNA24 : Firayi ministan na Pakistan ya bayyana hakan ne cikin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce wannan lokaci ne da ya kamata shugaba Macron ya kashe wutar da ta kunno kai da kuma rufe ƙofa ga masu tsaurin ra’ayi maimakon yin abubuwan da za su sake buɗe ƙofar tsaurin ra’ayi na addini.

Imran Khan ya ci gaba da cewa: Amma abin baƙin cikin shi ne Macron ya zaɓi tafarki kwaɗaitar da kyamar Musulunci ta hanyar sukar Musulunci maimakon sukar waɗanda suke aikata ayyukan ta’addanci shin musulmi ne, ko masu fifita fararen fata ko kuma ‘yan Nazi.

A farkon makon nan ne dai shugaban Faransa ya bayyana Musulunci a matsayin addinin da ke cikin rikici da tsaka mai wuya a duk faɗin duniya da kuma jingina ta’addanci ga musulmi. Wannan kalamai nasa dai yana ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga ɓangarori daban-daban na duniyar musulmi inda wasu ƙasashen musulmin ma suke kiran da a ƙaurace wa kayayyakin Faransan.

342/