21 Oktoba 2020 - 16:04
Iran: Sojoji Da Kuma Rundunar IRGC Zasu Fara Atisai Don Nuna Kwarewarsu Wajen Kare Kasar

Sojojin kasar Iran tare da hadin guiwa da dakarun kare juyin juya halin musulunci IRGC ta kasar za su fara wani atisai wanda zai mamaye kimanin rabin kasar da ga yau Laraba.

ABNA24 : Majiyar muryar JMI ta nakalto wata majiya ta na cewa Burgediya Janar Qader Rahimzadeh na rundunar Khatamul anbiya ne zai jagoranci atisayin.

An sanyawa itasayin suna Modafe’an-e Aseman-e Velayat 99, ko masu kare samaniyar waliyar 99 , kuma manufarsa itace bayyana karfin da sojojin kasar suke da ji na kare sararin samaniyar kasar.

Har’ila yau za’a gwada sabbin malamai wadanda sojojin kasar suka samu a baya-bayan nan.

342/