ABNA24 : Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake zantawa da tashar rediyon kasar Rasha a birnin Moscow, Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, Rasha ba ta da matsala kan kulla alaka tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila, amma da sharadin cewa hakan ba zai cutar da al’ummar Falastinu ba.
Ya ci gaba da cewa, suna girmama duk duk wani shiri na diflomasiyya tsakanin Isra’ila da wata kasa, amma idan bai yi hannuun riga da ka’idoji da dokokin da majalisar dinkin duniya ta shata ba.
Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka take matsa lamba akan gwamnatocin kasashen larabawa da suke yi mata biyayya sau da kafa, da kusa kulla alaka da Isra’ila a bayyane, domin yin amfani da hakan wajen cimma manufofi na siyasar gwamnatin Amurka mai ci a yanzu, da kuma tsamo Netanyahu daga matsalolin da ya shiga a Isra’ila.
342/