ABNA24 : Dr. Rauhani ya ci gaba da cewa; An sami wannan nasarar ce saboda kokarin diplomasiyyar Iran, sannan ya kara da cewa; Dauke wa Iran din takunkumin daya ne daga cikin sakamakon yarjejeniyar Nukiliyar Iran, don haka daga ranar Lahadi mai zuwa za mu iya saye da kuma sayar da makamai ga kowace kasa a duniya.
Shugaban na kasar Iran ya ci gaba da cewa; Muna ganin yadda ashararancin Amurka bai tsaya akan Iran kadai ba, ya shafi al’ummu da dama da suka hada da Afghanistan, inda kullum su ke cewa za su tabbatar da tsaro amma hakan ba ta faru ba.
Har ila yau, shugaban kasar na Iran ya yi ishara da Amurka da ta riya cewa za ta yi maganin Da’esh a Iraki da Syria, ba ta yi ba, alummun wadannan kasashen ne da kuma taimakon Iran su ka kawo karshen ‘yan ta’addar.
342/