ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto mataimakin gwamnan lardin na Ardabil da ke arewa maso yammacin kasar Iran ya na cewa jirgin ya fadi ne a kauyen Uzunteppe dake kusa da kan iyakar kasashen biyu.
Bahruz Nedae ya ce an fara gudanar da bincike don gano daga inda jirgen ya fito. Tun fiye da wata guda kenan kasashen Armenia da kuma Azarbejan suke fafatawa a tsakaninsu kan mallakar yankin Nagorno-Karabakh. Amma sau da dama makaman da suke musaya a tsakaninsu sukan fada cikin lardin Ardabil na kasar Iran.
342/