ABNA24 : A wata hira da yayi da jaridar kasar Austria mai suna Die Presse, yayin da yake amsa tambayar da aka masa dangane da batun lokacin da Iran take bukata wajen kera makaman kare dangi, babban daraktan hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya ce su ba lokacin da ake bukata wajen kera makamin suke la’akari da shi ba, suna la’akari ne da yawan taceccen yuraniyom ko kuma sinadarin plutonium da ake bukata ne wajen kera makamin. Don haka a halin yanzu dai Iran ba ta da wannan adadin.
Yayin da yake mayar da martani ga wadannan kalaman, jakadan Iran din a hukumar ta IAEA, Kazem Gharibabadi ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa batun lokacin da ake bukata da kuma adadin yuraniyom da ake bukata ma bai taso ba dangane da kasar da take gudanar da dukkanin ayyukanta karkashin kulawa da kuma sanya idon hukumar ta IAEA.
Jakadan na Iran ya ce ba haka ya kamata babban daraktan yayi magana ba, don kuwa ya san hakikin abin da ke faruwa a cibiyoyin nukiliyan na Iran.
342/