10 Oktoba 2020 - 12:43
​Hukumar Abinci Ta Duniya Ta Lashe Kyautar Nobel

Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta lashe lambar yabo ta Nobel, sakamakon gudunmawar da take bayarwa wajen yakar matsalar Yunwa a sassan duniya.

ABNA24 : Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da ake nasarar hukumar ta WFP a birnin Oslo na kasar Norway, shugaban kwamitin bada lambar yabon ta Nobel Berit Riess-Andersen, ya ce annobar corona ta kara tsananta halin yunwa da mutane suke ciki a wasu sassa na duniya.

Riess-Andersen ya kara da cewa, suna fatan ganin mutanen duniya sun karkata idanunsu domin ganin halin yunwa da wasu ke ciki a wasu kasashen duniya.

Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ita ce kan gaba wajen ayyukan jinkai a duniya, inda take taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci ga mutane sama da miliyan 690, dake fama da yunwa.

Matsalolin yake-yake da tashe-tashen hankula da fari na daga cikin abubuwan da suke jefa al’ummomi cikin matsanancin talauci da rashin abinci, kamar yadda kuma a wannan shekara bullar cutar corona ta taimaka wajen mayar da hannun agogo baya a harkokin noma da kasuwanci a duniya, wanda ya yi babban tasiri wajen kara tsanantar wannan matsala.

342/