ABNA24 : Shugaban na kasar Iran ya bayyana hakan ne a yayin da ya yi tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Azerbaijan, Ilham Aliyev, tare da bayyana kasar a matsayin kyakkyawar makwabciya.
Shugaba Rauhani ya kara da cewa; A tsawon tarihi da akwai alaka mai kyau a tsakanin al’ummun Iran da Azerbaijan ta fuskokin al’adu da kuma addini.
Har ila yau, shugaban na kasar Iran ya bayyana damuwarsa akan yadda ‘yan waje su ke tsoma baki a cikin rikicin kasashen biyu da hakan zai iya mayar da shi zuwa yaki na yanki.
A nashi gefen, Aliyev, ya yi godiya ga Iran saboda matsayar jami’anta akan abinda yake faruwa, da kuma yadda suke bayyana kasantuwar Azerbaijan dunkulalliyar kasa mai cin gashin kanta.
342/