ABNA24 : Ana fatan yarjejeniyar mai cike da tarihi za ta kawo karshen zubar da jinin da aka kwashe shekaru 17 ana yi a wannan kasa.
Yarjejeniyar dai ta tanadi bangarori guda takwas, da suka hada da mallakar filaye, biyan diyya ci gaban yankunan manoma da raba arziki da mulki da kuma komawar yan gudun hijira, akwai kuma shigar da mayaka cikin aikin soji
Wakilan daga gwamnatin rikon kwarya ta Sudan din, da jagororin ‘yan tawayen kasar, da jami’an diflomatisyya daga kasashen Chadi, Qatar, Masar, Da tarayyar Afrika da kuma MDD, na daga cikin wadanda suka halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar.
342/