ABNA24 : Khadib Zade ya kara da cewa wannan wani ci gaba ne a yakin da ake yi a kasar Yemen, kuma mataki ne na tattaunawa tsakanin yan Yemen su kadai.
Daga karshe Khadib Zade ya kammala da cewa akwai bukatar wannan tattaunawar ta ci gaba har zuwa lokacinda za’a dakatar da yaki a kasar ta Yemen.
A Ranar Lahadin da ta gabata ce jakadan MDD na musamman kan rikicin kasar Yemen Martin Griffiths ya bada sanarwan cewa bangarorin biyu sun amince su yi musayar fursinoni har guda dubu guda a karo na farko.
Tun ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015
ne kasashen Larabawa karkashin Jagorancin gwamnatin Saudiya suka farwa kasar Yemen
da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar.
342/