ABNA24 : Kasashen turai ne suka bukaci taron kwamitin kan kazamin fadan da ya barke tsakanin bangarorin biyu a yankin Karabakh, kamar yadda wasu majiyoyin diflomatisyya suka tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.
Dama kafin hakan kasashen duniya na ci gaba da kira ga kasashen na Armenia da Azerbaijan dasu tsagaita wuta tare da shinfuda hanyoyin shiga sulhu domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Rahotanni sun ce an samu hasarrar gwamman rayuka ciki har da na fararen hula a fadan da ya barke tsakanin kasashen biyu.
342/