ABNA24 : Tawagogin da suka hada data gwamnatin Tripoli dake samun goyan bayan MDD, da kuma Tobrouk zasu sake komawa teburin tattaunawar da suka soma a farkon watan Satumba.
Tattaunawar za ta maida hankali ne kan yadda za’a zabi jami’an da zasu jagoranci manyan mukamai na gwamnatin kasar.
Za kuma su duba yadda za’a iyakance mulki na tsakanin shugaban gwamnati da kuma shugaban majalisar da zatayi mulki.
A yanzu haka dai fira minista Fayez el Sarraj ne ke rike da wadannan mukamai.
342/