ABNA24 : Wata majiya a tawagar gwamnatin Yemen mai murabus data bukaci a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa an cimma matsaya ta musayar fursunoni 1,081 kuma nan da makwanni masu zuwa za’a aiwatar da yarjejeniyar, inda za’a sallami sojoji 400 ciki harda na kawancen da Saudiyya ke jagoranta, sai kuma mayaka daga bangaren ‘yan Houtsis 681.
Wasu bayanai na daban sun ce yau Lahadi ake sa ran kammala tattaunawar, inda kuma za’a sanar da yarjejeniyar da aka cimma, kuma daga cikin fursunonin da ake son sallama har da wani dan uwa ga shugaban kasar mai murabus Abedrabbo Mansour Hadi.
Game kuma da bukatar sakin Janar Nasser Mansour Hadi, ‘yan Houtsi sun jinkirta sakin nasa.
Idan dai har wannan musayar ta tabbata, zata iya kasance wata musayar fursunoni mafi yawa a tsakaninsu tun bayan yakin da barke a kasar a cikin shekara 2014.
Wannan dai na daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da bangaroron biyu suka cimma a shiga tsakanin MDD, a cikin shekara 2018 a kasar Sweden.
Bangarorin dai sunyi alkawarin musayar fursunoni kimanin 15,000 a tsakaninsu.
342/