26 Satumba 2020 - 15:35
Jam’iyyar Adawa Mafi Girma A Kasar Guinea Ta Bukaci ECOWAS Ta Shiga Tsakaninta Da Jam’iyya Mai Mulkin Kasar

Shugaban jam’iyyar adawa mafi girma akasar Guinea Conakry Cellou Dalin Dialo ya bukaci kungiyar kasashen raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta shiga tsakani don hana shugaban kasar mai ci Alpga Cone sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalti Dialo yana fadar haka a jiya Alhamsi. Ya kuma kara da cewa zai so kasashen yammacin Afirka su shiga tsakanin don ganin Alpha Conde bai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben ranar 18 ga watan Octobamai zuwa ba.

Dialo dan shekara 68 a duniya yay i takarar shugabancin kasar har sau biyu a baya tare da shi shugaban Conde kuma ya kasa kada shi.

Kungiyar ECOEWAS dai ta sha shiga cikin rigingimun siyasa na kasashen kungiyar don warware matsalolin da suke fama da su. Na baya-bayan nan shi ne juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Mali a ranar 18 ga watab Augustan da ya gabata.

342/