ABNA24 : Gwamna Obaseki ya dai doke abokin hamayarsa na Jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, kuma wannan shi ne karo na biyu da Obaseki ke doke Ize-Iyamu, amma lokacin Obaseki na APC, shi kuwa Ize-Iyamu yana a PDP.
Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki ya samu kuri'u dubu 307 da 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu kuri'u dubu 223 da 619 a ciikin adadin kuri'un da aka jefa 550,242
Ana dai kallon zaben na jihar Edo, tamkar wani zakaran gwajin dafi ne tsakanin APC da PDP.
342/