ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Rasha a hukumar Mikhail Awliyonuv yana fadar haka a shafinsa na twitter . Ya kuma kara da cewa an gudanar da taron ne a babban dakin taro na hukumar saboda hana yaduwar korona a tsakanin mahallata taron.
Agendar taron gwamnonin dai sun hada da yarjejeniyar JCPOA ta kasar Iran da kuma batun harkokin tsaro a yankin kudancin Asia.
Har’ila yau za ta tattauna dangane da matakan da kasar Iran take dauka na jingine wasu alkawulan da ta dauka a yarjejeniyar JCPOA kamar yadda maddoji na 26 da kuma 36.
342/