ABNA24 : Muhammad Abdussalam ya yi Allah wadai da babbar murya akan yadda kungiyar hadin kan kasashen larabawan ta ki yarda da bukatar Palasdinawa.
Kakakin na kungiyar Ansarulalh ya kuma ce; Al’ummun wannan yankin suna a raye, kuma kasashen da su ka yi tir da wannan matsayin na kungiyar hadin kan kasashen larabawa a cikin kungiyar su ne abin dogaru da jingina wajen goyon bayan hakkin palasdinawa.
A tsakiyar mako mai karewa ne dai kungiyar ‘yanto Palasdinu ta PLO ta bakin sakatarenta, Sa’ib Uraiqat ta yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar Larabawan idan har ta amince da daftarin kudurin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gagabatar mata akan hulda da HKI.
342/