ABNA24 : Babban Bankin kasar ya ce yana shirin haramta amfani da kudaden kasashen waje a duk fadin kasar, domin kaucewa kara tabarbarewar darajar kudin kasar na pound akan dalar Amurka.
Wannan dai ya biyo ne bayan tashin gwauron zabi da kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi suka yi a kasar a ‘yan watannin nan.
A ranar Alhamis, kwamitin sha’anin kasuwanci na majalisar dokokin Sudan ta Kudu, ya gayyaci gwamnan babban bankin kasar Gamal Abdallah Wani, da Ministan Kudi Garang Mabior da kuma mataimakin kwamishinan hukumar tara haraji ta kasa Erjok Bullen, domin su amsa tambayoyi akan faduwar darajar kudin kasar na pound.
342/