ABNA24 : A Wani taron manema labaru da ‘yan hamayyar su ka yi, sun yi tir da yadda ake gudanar da tantance sunayen wadanda su ka yi rijistar zaben, su na masu bayyana dalilinsu da cewa an hana wakilansu a hukumar zabe ta ‘CENI’ samun bayanan da suke cikin na’ura mai kwakwalwa da take dauke da sunayen wadanda aka yi wa rijistar.
Matakin na kin amincewa da tantance sunayen masu yin zaben, shi ne irinsa na farko a tarihin siyasar jamhuriyar Nijar, kamar yadda shafin “ Actu Niger’ ya bayyana.
Wani Karin dalilin na kin lamunta da yadda tantance rijistar ke gudana shi ne yadda aka kayyade kwanaki biyar kadai na yin aikin, ta yadda ‘yan hamayyar su ka bayyana cewa; a kasar Togo da yawan mutanenta bai kai na Nijar ba, an dauki wata guda cur ana yin aikin.
Kawancen hamayyar siyasa na neman mafita, wanda a takaice ake kira ( CAP), tun yanzu ya sanar da cewa; ba zai amince da sakamakon aikin tantancewa rijistar masu zaben ba.
342/