10 Satumba 2020 - 09:53
Iran:Daliban Makarantun Addini A Qom Sun Yi Allawadai Da Wulakanta Manzon All..(s)

Daliban makarantun addini a birnin Qum da ke kudancin birnin Tehran sun fito zanga-zangar yin All..wadai da wulakanta manzon All…(s) da wata jaridar kasar Faransa mai suna Charlie Hebdo ta yi a baya-bayan nan.

ABNA24 : Daliban sun gudanar da zanga-zangar lumana zuwa gidan marigayi Imam Khomaini (q) wanda ya kafa jumhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Qum.

Daliban sun yi All..wadai da MDD kan shirun da ta yi kan wannan walakancin, sannan sun bukaci a hukunta wadanda suka yi wannan aikin.

Kafin haka dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce ba ya ganin wani laifi a abinda jaridar “Charlie Hebdo” ta yi don a kasar Faransa, a ganinsa mutane su na da ‘yancin fadin albarkacin bakinsu.

342/