10 Satumba 2020 - 09:48
​‘Yan Majalisar Dokokin Burtaniya Sun Yi Allawadai Da Takura Wa Musulmi A China

Fiye da ‘yan majalisar kasar Burtaniya 130 ne suka sanya hannu kan wata wasika da ke yin tir da Allawadai da takurawa musulmin Igoir da gwamnagtin kasar China take yi.

ABNA24 : Rahotanni daga kasar Burtaniya sun ce, ‘yan majalisar dokokin kasar wadanda akasarinsu daga jam’iyyar Labour adawa suke, sun sanya hannu kan wata takarda, wadda suka yi kakkausar suka kan cin zarafin musulmi da gwamnatin China take yi.

‘Yan majalisar sun aike da wannan takadarda zuwa ga jakadan kasar China a London Liu Ziaoming, domin ya isar da wannan sako ga gwamnatin kasarsa.

A cikin watan Yulin day a gabata, sakataren harkokin wajen Burtaniya ya zargi gwamnatin China ta takura wa musulmin Igoir, tare da killace fiye mutane miliyan daya daga cikinsu a wani wuri mai kama da gidan kaso.

342/