9 Satumba 2020 - 10:49
​Rauhani: Iran Ba Za Ta Taba Rusuna Wa Halayyar Dabanci Irin Ta Amurka Ba

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa; Tun bayan da Amurkan ta fice daga cikin yarjejeniyar Nukiliya da kuma keta kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231, ta mayar da hankali wajen kakaba wa al’ummar Iran takunkumi na zalunci a cikin shekaru biyu da rabi.

ABNA24 : Shugaban na kasar Iran ya kara da cewa; Al’ummar Iran ba ta taba, kuma ba za ta taba rusunawa a gaban masu girman kai ba , kuma tarihi ya yi wa al’ummar Iran din sheda akan hakan.

Shugaban kasar ta Iran wanda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen kasar Switzerland, Ignazio Cassis.

Wani sashe na bayanin shugaban kasar ta Iran ya kunshi cewa; A yanzu an wayi gari Amurkawa sun gane cewa sun yi kuskure da su ka fice daga cikin yarjejeniyar Nukiliya, kuma ba za su cimma manufofinsu ba ta hanyar yi wa Iran matsin lamba.

342/