ABNA24 : Jam’iyyar ANC mai mulki da gidauniyar Mandela duk sunyi tir da sukan.
Kalamman da ake alakantawa dana suka, sun fito ne daga cikin wani sabon littafin tsohon lauyan shugaban na Amurka Trump, cewa da Michael Cohen, da aka ce za’a fitar yau Talata.
A cikin littafin, Mr Cohen ya yi ikirarin cewa Trump ya yi tsokacin nuna kyama kan Nelson Mandela, inda yake cewa tsohon shugaban na Afirka ta Kudu ba "shugaba ba ne".
Mr Cohen, ya ce akwai inda Trump, yake cewa a fada masa wata kasa da wani bakar fata ya shugabanta, wacce bata koma masai ba, saidai fadar White House ta musanta batun tare da cewa lauyan karya ce yake yi.
342/